"Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna." (1 Yahaya 4:11). Yahaya ya rubuta har sau goma sha uku cikin wasikun shi guda uku kalmomin karfafawa wa masu karatu domin su kaunaci juna. MUNA KAUNA DOMIN SHI NE YA FARA KAUNAN MU / 1 YAHAYA 4:19 Muna iya kaunan juna domin mu ma mu samu kauna daga Allah, wanda Ya ba da ɗan Shi haɗaya domin mu. "Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa...